Zamu Hana shan giya a katsina ~Masari

Majalisar dokokin jihar Katsina ta koka sosai dangane da yadda ake samun yawaitar wuraren sha da kuma saida giya da sauran kayan maye are cikin garin Katsina.

Majalisar ta bayyana matsayar tata ce biyo bayan wani kudurin gaugawa da Dan majalisa mai wakiltar karamar hukumar Katsina Hon. Aliyu Abubakar Albaba ya gabatar are farko watan nan inda yace ya kamata a fadawa gwamnati ta tsawatar.

Da yake gabatar da kudurin, Hon Albaba ya bayyana takaicin sa ga lamarin musamman duba da cewa akwai dokokin da suka hana wadannan laifukan tun kusan shekaru Ashirin da suka gabata.

Honorable

Albaba ya kara da cewa yana kira ga majalisa cikin gaugawa da ta tura wannan kudiri ga gwamnatin jiha domin daukar mataki.

Bayan tattaunawa mai tsawo akan kudirin, daga karshe majalisar ta mika ma kwamitin kula da harkokin addini na majalisar karkashin jagorancin Honorable Mustapha Yusuf Jibia da ya binciko ya kuma kawo mata da rahoto cikin sati uku.

rahoton katsina post..

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *