Zamu kashe duk wani Dan bindiga da muka Kama a jihar Filato ~Gwamna Lalong.

Gwamnan jihar Filato, Simon Bako Lalong, ya gargadi masu garkuwa da mutane da su bar jihar Filato domin duk wanda aka kama kuma aka samu da laifi zai fuskanci hukuncin kisa.

Gwamnan yana magana ne a babban cocin Katolika da ke karamar hukumar Shendam a jihar.

Ya kuma tabbatar wa da ‘yan jihar cewa gwamnati za ta kara kaimi wajen yaki da duk wani nau’in laifuffuka, musamman garkuwa da mutane wanda ya zama barazana ga zaman lafiya da tsaron al’ummar jihar da ma sauran sassan kasar nan.

Gargadin

bai rasa nasaba da sace-sacen da ake fama da shi a wasu sassan jihar a kwanakin baya.

A ranar 26 ga Disamba, 2021, Daily Trust  ta rahoto yadda aka yi garkuwa da babban sarkin garin Gindiri na karamar hukumar Mangu, Charles Mato Dakat a gidansa kuma aka sake shi bayan ya kwashe kwanaki hudu a tsare.

Hakazalika, a jajibirin sabuwar shekara, an yi garkuwa da wani dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP, Dr Kemi Nshe a gidansa da ke garin Shendam.

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *