Zamu sake fitar da ‘yan Nageriya mutun milyan ashirin da biyar 25m daga kangin talauci ~Cewar Farfesa Osinbajo

Mataimakin shugaban Ƙasar Nageriya farfesa Yemi Osinbajo yace shirin Hukumar zuba hannun jari ta ƴan Najeriya mazauna ƙasashen waje wato- NDIS na ɗaya daga cikin wata hanya Mai mahimmanci da zata kawo zuba hannayen jari a Ƙasar.

Osinbajo ya bayyana haka a lokacin taron Hukumar cigaban ƴan Najeriya mazauna ƙasashen waje NDIS karo na 4 na wannan shekara ta 2021.

Mataimakin Shugaban Ƙasa yace hakan zaiyi sanadiyar a fitar da ‘ƴan Najeriya Miliyan 25 daga ƙangin Talauci a shekarar 2025.

Taron

Daya gudana ranar Talata a ɗakin taro na shugaban ƙasa dake Villa Abuja.

Osinbajo Wanda ya samu wakilcin Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha yayi nuni dacewar an ƙirƙiri NDIS domin samar da zuba hannun jari a Najeriya.

Osinbajo ya bayyana cewar manufar Gwamnatin Buhari shine a inganta kuɗaɗen shiga a ƙasar.
Yace gwamnatin a shirye take domin samar da ayyukan yi ga matasa Yan Nageriya.

One thought on “Zamu sake fitar da ‘yan Nageriya mutun milyan ashirin da biyar 25m daga kangin talauci ~Cewar Farfesa Osinbajo

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *