Zamu taimaki kasar Niger domin kawo karshen ta’addanci a kasar ta Niger ~Cewar Shugaba Buhari

Shugaba kasa Muhammadu Buhari ya yi alkawarin tallafawa Najeriya domin kawo karshen ta’addanci a Nijar da sauran kasashe makwabta.

“Najeriya za ta ci gaba da tallafa wa makwabtanmu a kokarin hadin gwiwa na yaki da ta’addanci,” in ji shi a ranar Asabar.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne biyo bayan kisan gillar da ‘yan ta’adda suka yi wa mutane 69 a Nijar. ‘Yan ta’addan sun aikata munanan laifuka a kan iyakar Nijar da Mali da Burkina Faso, inda suka kashe mutane cikin ruwan sanyi. Daya daga cikin wadanda suka jikkata har da wani magajin gari.

Da

yake jajanta wa shugaban kasar Nijar Mohammed Bazoum, Mista Buhari ya ce “Muna taya ku jajen wannan mummunan lamari,” kuma wannan zai karfafawa sauran “shugabannin Afirka da cewa kada su bar wani abu ba tare da saukar mataki ba a kuma karya wadannan abokan gaba na bil’adama.

Sakon ta’aziyyar Buhari na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Garba Shehu, mai magana da yawunsa ya fitar.

Ya bayar da shawarar yin hadin gwiwa a tsakanin kasashen da ke fama da tashe-tashen hankula don magance matsalar rashin tsaro.

“Lokaci ya yi da za mu hada karfi da karfe don murkushe wadannan muggan laifuka wadanda ke haifar da babbar barazana ga zamantakewa da tattalin arziki a kasashenmu.”

Mujallar da ke Landan, The Economist a editanta na Oktoba 23 mai taken “The  The Crime Scene at the Heart of Africa”, ta bayyana Mista Buhari a matsayin wanda ba shi da kwarewa kuma ba shi da basira wanda gazawarsa wajen magance cin hanci da rashawa ya kara tabarbarewar tsaro a Najeriya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *