Zamu yi duk Abinda ya dace domin warware matsalar data hana aikin wutar mambila ~Cewar Gwamnatin Buhari.

A wani martanin Fadar Shugaban Kasa daga Mataimakin Shugaban kasa na musamman Kan Sabbin kafafen sada zumuntar Zamani da yake martani ga ‘yan Nageriya Yana Cewa dalilin dayasa ban magana ba a Kan Batun ba shine Na shafe mafi kwanaki biyu a kan hanya, wannan shine dalilin da ya sa ban yi tsokaci game da shirin Binciki na BBC Hausa na baya -bayan nan ba kan aikin samar da wutar lantarkin Mambilla, ko lokacin da na isa inda na nufa kuma a shirye nake nayi martani Amma sai na gano Malam Garba Shehu. , Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban kasa kan Kafafen Yada Labarai Tuni ya yi tsokaci kan batun da ke yawo kuma abin da ya fada daidai ne abin da ya faru, martaninsa ya isa, don haka ba zan kara komai ba.

Bashir

Ahmad ya Kara da Cewa Na fahimci dukkanmu mun damu da aikin musamman saboda muhimmancinsa ga ci gaban zamantakewa da tattalin arzikin mu.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnatin sa ba za su taba yin watsi da wani aiki mai irin wannan muhimmanci ga al’ummar Najeriya ba tare da wani dalili ba. Lokacin da na zanta da shi kan batun, sabon Ministan wutar lantarki, Engr. Abubakar D. Aliyu ya shaida min cewa zai yi duk abin da zai yiwu don ganin an warware dukkan batutuwan da suka dabaibaye aikin don amfanin Najeriya da al’ummarta.

  • Bashir Ahmad

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *