Zan cigaba da sadaukar da kaina ga matasa domin Samar masu da sana’o’in dogaro da Kai ~Sanata Uba

A daidai wannan Lokaci da muke fama da Matsalar ta’addanci a Nageriya musamman ma arewacin Nageriya, tabbas ana bukatar Shugabanni mu su maida Hankali wajen samar da ayyukan yi ga matasa domin kawo karshen barazanar tsaro musamman idan mukayi duba da yadda rashin ayyukan ke tilastawa matasan mu shiga harkokin ta’addanci ba tare da suna so ba, a daidai wannan yanayi da muke ciki dole ne muyi godiya tare da jinjinawa Sanata Uba sani wakilin kaduna ta tsakiya a majalisar dattijan Nageriya a kokarinsa na samawa matasa hanyoyin dogaro da Kai.

Binciken

masana na duniya ya tabbatar da Cewa Samar da hanyoyin dogaro da Kai ne ka’dai ka iya Kawo Karshen ta’addanci a Cikin Al’umma.

Sanatan ya mai da Hankali wajen gina cibiyoyin koyon sana’o’i ciki harda Samar da Cibiyar koyar da na’ura Mai kwakwalwa ta zamani (Computer) domin koyon hanyoyin dogaro da Kai ta Hanyar fasahar zamani.

Sanatan yana kokarin koyar da matasa dabarun kiyon zamani wa’yanda suka ha’da da kiwon kifi kaji da Sauransu duk domin kawo karshen Zaman kashe wando ga matasan mazabarsa.

Bayan Haka Sanatan na kokarin Samar da jarin kuɗaɗe masu tarin yawa ga Al’ummar mazabar Cikin harda mata da Tsofaffi.

Wasu da dama sun rabauta da jarin Milyan biyar-biyar 5m zuwa milyan goma-goma 10m domin dogaro da kai.

Sanatan yana biyawa dalibai kuɗaɗen jarabawa domin samun sauƙin ku’din karatu da samun dama shiga Makarantu na Gaba sakandiri a duk fa’din jihar kaduna.

Ire iren wannan ayyukan sune Suka dace da matasanmu na yanzu a daidai wannan Lokaci da muke fama da Matsalar ta’addanci a wannan Kasa tamu ta Nageriya mai albarka.

Sanata Uba sani na daga Cikin jerin ‘yan majalisar da suka samu Lambar yabo amatsayin ‘yan majalisar mafiya tarin ayyukan tare da Kai Kudri majalisar domin ganin Al’ummar da suke wakiltar ta kubutar daga Zaman kashe wando da kangin talauci.

Sanata Uba sani ya lashin tokobin cigaba da sadaukar da Kai ga Al’ummar da yake wakiltar domin ganin sun shiga yanayin walwala da annashuwa musamman a wannan Lokaci da yake wakiltar su a majalisar dattijan Nageriya. Daga Ibrahim Umar Musa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *