Zan cika duka alƙawarukan dana ɗauka a loƙacin zaɓe- Buhari

Zan Cika Duka Alƙawarukan Dana Ɗauka Loƙacin Zaɓe- Buhari

Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari ya tabbatarwa da ƴan Najeriya zai cika dukkan alƙawarukan da ya yi musu tun daga shekarar 2015

Shugaba Buhari ya bada wannan tabbacin a ranar Juma’a a loƙacin da ƙungiyar mago bayansa da mataimakinsa mai suna ‘Muhammadu Buhari and Osinbajo dynamic support group’ su ka ziyarce shi a gidan gwamnati

Ƙungiyar ta je Villa ne domin gabatar da littafin data wallafa wanda ya ke ƙunshe da nasarorin da gwamnatin Buhari ta cimma cikin shekaru biyar.

“Sakamakon

jajircewar wannan gwamnati shine silar wallafa wannan littafin sannan ina da yaƙinin da fatan ƴan Najeriya a kodayaushe suna ganin irin nasarorin da wannan gwamnatin ta cimma cikin shekaru biyar” in ji Buhari

Daga Mutawakkil Gambo Doko

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *