Zan dora daga inda Buhari ya tsaya ~Cewar Bola Tinubu.

Bola Tinubu, tsohon gwamnan Legas kuma jigo a jam’iyyar All Progressives Congress na kasa, ya ce zai tsaya takarar shugaban kasa a 2023 domin gina tubalin gadon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Mista Tinubu, wanda ya ziyarci Mista Buhari domin tattaunawa kan burinsa na siyasa a ranar Litinin, ya bayyana hakan ne bayan ganawarsa da shugaban.

“Ina da kwarin guiwa da hangen nesa, da ikon yin mulki, gina kan ginshikin shugaban kasa, da kuma inganta Najeriya wanda na yi kamar hakan da jajircewa a jihar Legas,” in ji Mista Tinubu. “Kun ga wannan ƙwarewar da kuma ikon juya abubuwa abin da zanuyi anan matakin kasa inji shi.

Advertisements

2 thoughts on “Zan dora daga inda Buhari ya tsaya ~Cewar Bola Tinubu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *