Zan kawo karshen ta’addancin zan Tabbatar na biya bashin da ake bin jihar kaduna idan na zama Gwamna ~Shehu sani

Tsohon Sanatan Kaduna ta tsakiya Shehu sani ya bayyana Ajandarsa idan ya zama Gwamnan Jihar Kaduna a zaben 2023 Mai Sanatan ya Bayyana hakan a shafinsa na Facebook Yana Mai Cewa Ajandar Talakawa Na Jihar Kaduna.
2023-2027

  1. Kawo karshen ‘yan fashi da ta’addanci da kuma tabbatar da rayuwar al’ummarmu ta hanyar ba da goyon baya da fasaha ga dukkan jami’an tsaro da ke jihar.
  2. Hada kan Al’ummar Arewa da Kudancin Kaduna domin samun zaman lafiya, daidaito, adalci da wadata.

3.Tabbatar

da biyan bashin jihar.
  1. Sake dawo da masana’antu na jihar, sake farfado da masana’antun da suka mutu, da kuma gagarumin tallafi ga kanana da matsakaitan masana’antu.
  2. Samar da ababen more rayuwa na yankunan karkara da aka yi watsi da su.

6.Soke budaddiyar kudade da boye kudade da kuma kudaden da ake biya a makarantun gwamnati da asibitocin gwamnati.

7.Massive and mechanized agricultural scheme and the agro allied industries domin a kalla gano amfanin noma na jihar.

8.Kafa sabbin jami’o’i biyu na likitanci, Injiniya da ICT.

9.Ceto Bangaren Wasanni da Maido da Kaduna zuwa saman Teburin Wasanni a Kasar nan.

  1. Haɗin kai da tallafawa ƙungiyoyin addini da cibiyoyin gargajiya don tsaro, zaman lafiya da ci gaba.
  2. Katafaren ginin gidaje da kafa garuruwan tauraron dan adam a Zaria,Kafanchan da Kaduna.

12.Wasu muhimman abubuwan da zan yi na kiyaye kaina a yanzu.

INSHA ALLAHU
DA IZININ ALLAH.
Inji Sanatan

Kawo yanzu Shehu sani Yana Shan Suka daga Al’umma da dama tun Bayan Daya furta Kalaman Cewa zai gyara tabargazar Malam Nasiru El Rufa’i.

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *