Zanga makara kunyar da zai tallata Jonathan idan ya koma Jam’iyar APC a zaben 2023 ~Cewar Tambuwal

Gwamnan jihar Sokoto Aminu Tambuwal ya gargadi tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya kuskura ya ce zai koma APC domin idan yayi haka ya jefa kan sa ne cikin buhun kaya.

Idan yayi haka, ina tabbatar muku da cewa su kan su APC din zanga yadda za su tallata shi, bayan irin kalaman da suka yi akan sa kafin zaben 2015. zai zama kamar abin da ya faru a zaben jihar Edo tsakanin tsohon gwamna Adams Oshiomhole da dan takarar APC Ize-iyamu wanda ya tallata.

Idan ba a manta ba, Ize-Iyamu da Oshiomhole ya tallata shine ya a baya ya yi wa ragaraga da buhun suka iri-iri a lokacin da yake tallata Osigie wanda a lokacin yana APC ne. Daga baya kuma ya zo yan so ya kwarzanta Ize-Iyamu dan sun yi hannun riga da Osagie wanda ya koma PDP, sai ya koma kuma wanda ya ragargaza a baya shiune yake tallatawa,

” Mutane za su koma baya ne su zakulo irin kalaman da suka yi akan Jonthan da mulkin sa a baya. haka mu a PDP za mu yi shikenan ya ishe mu. Sauran kuma jama’a da kansu za su yanke hukunci.

” Shawara ta ita ce kada Jonathan ya koma APC, ya hakura a PDP kawai a ci gaba da bugawa da shi. Nan ne zai fi zama masa kwanciyar hankali. Duk ma abinda yake nema a siyasa ya neme shi a PDP din, cikin mutuncin sa.

Sannan kuma a karshe Tambuwal ya yi kira ga yan uwansa ‘yan siyasa da su ke APC har yanzu su dawo tafiyar su a hadu a farfado da PDP tare.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *