A karon farko mutane biyu sun kamu da sabuwar cutar Omicron a Nigeria. ~Cewar NCDC

Daga | Ya’u Sule Tariwa,

Cibiyar magance tare da shawo kan annoba ta ƙasa wato NCDC ta tabbatarda cewa an samu mutane biyu ɗauke da sabuwar cutar da ake kira Omicron a Nigeria.

NCDC ta bayyana cewa sun gano hakan ne bayan da suka fara gwaji akan matafiya da suke shigowa Nigeria daga ƙasashen ketare.

Jiya Laraba ne aka fara samun masu ɗauke da cutar a faɗin Nigeria.

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *