An sake kashe mutun ‘daya an Kuma sace mutun sittin da takwas 68 a jihar Niger.

An kashe wani mafarauci yayin da aka yi garkuwa da mutane 30 a kauyen Zazzaga da ke karamar hukumar Munya ta jihar Neja.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Monday Bala Kuryas ya tabbatar wa da majiyarmu faruwar lamarin.

Ya ce lamarin ya faru ne da karfe 2 na safiyar ranar Laraba, inda ya kara da cewa, “ tuni ‘yan sanda suna bin maharan domin ceto wadanda aka yi garkuwa da su ba tare da sun ji wani rauni ba.

Sai

dai sakataren karamar hukumar Munya James Jagaba ya shaidawa wakilinmu ta wayar tarho cewa an yi garkuwa da mutane 68 da suka hada da mata da kananan yara.

“Sun zo da yawa a lokacin da al’ummar ke barci kuma suka mamaye al’umma. An kashe mutum daya, an harbi uku yayin da aka yi garkuwa da mutane 68,” inji shi.

Wata majiya daga unguwar ta ce ‘yan bindigar sun yi ta kai farmaki ne daga gida zuwa wancan.

“An harbe wani mafarauci ne a yayin da ake gwabzawar da Yan bindigar. Ba mu san inda mutanen da aka sace suke ba. Amma an baza jami’an tsaro da suka hada da ‘yan sanda da sojoji da ’yan banga a cikin al’umma,” inji shi.

Tabarbarewar tsaro a kasar dai ya kara dagulewa duk da tabbacin da hukumomin kasar suka sha yi.

Idan Baku manta A ranar Litinin din da ta gabata, sakataren gwamnatin jihar Neja ya ce al’ummomi biyar a karamar hukumar Shiroro na karkashin ikon ‘yan Boko Haram.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *