KIWON LAFIYA: Wata Likita mai suna Esther Nwachukwu ta shawarci mata akan su rinƙa yin fitsari aƙalla mintuna 30 bayan tarawa.

Likitoci sun bayarda shawara musamman ga ƴaƴa mata da su rinƙa yin fitsari aƙalla mintuna 30 bayan jima’i.

Wata ƙwararriyar Likita mai suna Esther Nwachukwu ce ta wallafa wannan faɗakarwa a shafinta na sada zumunta, Twitter.

Ta bayyana cewa, batun wai idan mace tayi fitsari bayan saduwa da namiji zai sanya ciki ya zube duk ƙarya ne.

Kuma ta ƙara da cewa, babban dalilin da ya sanya Likitoci suke shawartar ƴaƴa mata da su rinƙa yin fitsari aƙalla mintuna talatin bayan tarawa shine domin hana ƙwayayyakin cututtuka samun wurin shiga gangar jiki.

Likitar,

tayi bayani tare da alƙawarin cewa cikin rubutu na gaba zata kammala tare da ƙara wayar da ƴan’uwanta mata game da wannan al’amari.

Rahoto | Ya’u Sule Tariwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *