Sumbata Kiss na Karin Tsawon rai ga bil’adama ~Binciken masana.

Sumbata wata hanya ce da masoya ke amfani da ita wajen nuna soyayyar su ga wadanda suke so.

Ba ya masoya ba ka’dai hatta iyaye ma kan yi amfani da wannan hanya domin nuna soyayyar su ga ‘ya’yan su.

Wata marubuciya da masaniyar abincin dake inganta garkuwar jiki dake kasar Amurka Jeena Schreck ta bayyana wasu hanyoyin da Sumba ke inganta lafiyar mutane.

Ga hanyoyin

 1. Sumbata na Kara dankon soyayya a tsakanin masoya

Sumbata musamman tsakanin masoya na cikin hayoyin dake taimaka wa mata wajen amincewa da namiji wajen yin jima’i ko aure.

  start="2">
 1. Faranta rai

Sumbata hanya ce dake faranta wa mutum rai yana kuma taimakawa wajen rage gajiya a jiki.

An ce gamsuwar da ake samu a lokacin da ake sumbartar masoyi kusan dai-dai yake da irin dadin da wanda ke maskewa da Heroin.

 1. Inganta fatar mutum

Musamman ga mata sumbatar masoyi na kara hasken da annuri a fuskar mace ta rika sheki tana

 1. Sumbata na taimaka wa mutane da dama wajen samun gamsuwa kafin jima’i. Sannan yana taimaka wajen inganta sha’awar yin jima’i ga masoyi da masoyiya.
 2. Sumbata na kara tsawon Rayuwa: Wani sakamakon bincike da Arthur Szabo ya gudanar ya nuna cewa sumba na kara tsawon rayuwar mutane a duniya.

Sakamakon binciken ya nuna cewa muddin namiji na sumbar matarsa da safe kafin ya tafi wurin aiki yana kara tsawon rayuwarsa domin zai tafi aiki cikin jin dadi da anashuwa.

Duk da haka akwai wasu hanyoyi da suka nuna cewa sumba na cutar da lafiyar mutane inda haka ya zama dole mutane su rika yin hatara da irin mutanen da suke Sumba.

Cututtuka shida da ake kamuwa da su ta hanyar sumba.

 1. Tarin fuka
 2. Mura da tari.
 3. Kwayoyin ‘Bacteria’ dake kama hakora da saka warin baki.
 4. Hepatitis B
 5. Cututtukan sanyi kamar ‘Herpes’, ‘Gonorrhea’, Syphilis da sauran su.
 6. Cutar ‘Meningococcal’: Cutar na kama da cutar sankarau domin yana kama kwakwalwa da kashin baya sannan ana kamuwa da shi ta hanyar yin Sumba
  An wallafa wannan labari a mbg love premium time.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *