UNICEF ta gargaɗi ƴan Nigeria akan su gujewa yin tsiguno a bainar Jama’a.

Daga | Ya’u Sule Tariwa,

Shugaban hukumar kula da haƙƙin ƙananan yara UNICEF reshen Jihar Enugu, Dr Brahim Conteh ya gargaɗi mutane akan illar yin tsuguno a ko’ina.

Dr Conteh ya bayyana hakan ne ayau Juma’a yayin gudanar da bikin “Ranar Ruwa” wadda majalisar ɗinkin Duniya ta ware.

Ya kuma ƙara da cewa, bayan wani bincike wanda yana gab da kammaluwa game da ƴan Nigeria, adadin masu anfani sa sinadarin wanke hannu bayan tsuguno wanda hukumar lafiya ta tanada na musamman bai wuce kaso 23 cikin ɗari ba.

Kuma aƙalla mutane 46 suke yin tsiguno a bainar sahara.

A

jerin jadawalin Jihohin da ya lissafo waɗanda aka fi yin bahaya a bainar Jama’a sun haɗa da; Kwara, Plateau, Ebonyi, Abia, Zamfara da kuma Jihar Akwa Ibom.

Ya kuma tabbatar da cewa, Nigeria tana samun nasarori ta fannin samar da ababen tsaftace wuraren tsuguno (toilet) tare da abin wanke hannu domin hana yaɗuwar cututtuka.

A ƙarshe, Mista Conteh ya bayyana cewa ya kamata a ƙara himma wajen tabbatarda cewa kowa yana amfani da wadatattu tsaftataccen matsuguni domin taƙaita yaɗuwar cututtuka a tsakanin al’umma

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *