•Cin Zarafin Mata a wurin turawan yamma. •Duk Second 9 sai an doki Mace a America.


Mata mutane ne (Ba kamar yadda turawan yamma suke dauka ba cewa ita ba mutum bane kuma ita ba dabba bane, kawai dai tana tsakiya) kuma halitta ne mai daraja da daukaka, ba tare da la’akari da cewa Musulma ce ko akasin haka ba. Don kuwa Manzon Allah (SAW) yace: “Babu Mai girmama su (Mata) sai Mai girma; babu mai wulakanta su sai Kaskantacce (Wulakantacce)” Au kama Qala.

Masu hikima suna cewa “Mace itane Rabin al’umma; Kuma ita ta haifi dayan Rabin” dan haka idan babu ita babu al’umma.

Amma

yau matan mu musulmai sun rudu da Nazariyya ko Ideology na turawan yamma inda suka daukesu a matsayin ababen koyin su akan wasu al’amuran da mu tuntuni addinin mu ya tsara mana yadda zamuyi handling dinsu cikin ruwan sanyi, amma sai suke ganin an tauye masu hakin su a matsayin su na mata, dan haka aka kawo masu tallar nema masu ‘yanci wato “LIBERATION” suka sa kudin su suka siya, alhali su wadancan da suka kawo masu tallar sunfi su dandanan kudar su a hannun mazajen su, amma sai suna boye nasu, a gefe daya kuma suna tunzura matan mu musulmai.

Duk da dai da akwai laifin wasu mazajen namu, domin kuwa Babu wani addini Samawiy da ya yarda da cin zarafin mata, dan haka ba kada wani lasisi da zaka samu ‘yar mutane (Matarka) kayita duka kamar Jaka. Hakan ne ma yasa Sarkin Kano na 14, Khalipha Malam Muhammadu Sanusi II, yace “Duk Macen da Mujinta ya dake ta ta rama” duk da dai ni bana tare dashi akan cewa ta rama, ni a ganina shine: Madadin ace ta rama gwara dai ace ta dauki duk matakan da suka dace kar ta bari dukan ya tafi a banza.

•Dukan Mata a Kasar America:- A Kasar America mata suna dandana Kudar su a hannun mazajen su domin kuwa alkaluma sun nuna cewa “Kesa-kesan da (Cases) da ake samu a America kashi 77 cikin 100 na dukar mata ne”
Kamar yadda kididdiga ta tabbata daga Family Violence Prevention Fund shine: duk Dakika tara (Wato Second 9) sai an doki mace a America.

Hakanan Federal Bureau of Investigation (FBI) sun tabbatar da cewa kashi 25 (25%) na masu yunkurin kisan kansu (Suicide attempt) mata ne da suke shan shegen duka (Extreme Beat) daga mazajen su.

Sannan yazo a cikin wata mukala mai taken “Why Men hurt the Women they like” cewa a Kasar America duk Shekara ana samun Mata Sama da Miliyan Daya (1 Million) da suke bukatar kulawar likita sakamakon dukan da suka sha a hannun mazajen su, sannan duk rana ana samun mata Hudu da suke mutuwa sakamakon dukar.

A wani bincike da American National Office for Psychological Health suka gabatar sun tabbatar da cewa kashi 17 (17%) na matan da ake dauka da Ambulance wadanda suka sha duka ne a hannun Mazajen su.
Janice Moor Coordinator ce ta National Solidarity against Domestic Violence Organization dake America ta tabbatar da cewa “A America duk Shekara ana samun mata sama da Miliyan 6 da suke shan Shegen duka a hannun mazajen su.

Ita kuma US TIME MAGAZINE ta tabbatar da cewa a cikin matan nan miliyan 6 da suke shan dukan ana samun kimanin mata dubu Hudu (Four thousand) da suke mutuwa Sakamakon Wannan dukar.

•Dukan Mata a Kasar Germany:- Prof. Ibrahim Ahmad Aliyu a wani littafi nasa ya tabbatar da cewa duk Shekara ana samun akalla mata Million daya da suke shan duka a hannun mazajen su.

Haka ma German Family Minister Franziska Giffey ya bayyana cewa kowace awa daya (1hrs) cikin awa 24 ana samun dukan mata a Kasar Germany.

•Dukan Mata a Kasar Faransa:- A Kasar Faransa duk Shekara kimanin Mata Miliyan 2 ne suke shan duka a wurin Mazajen su. Hukumar ‘yan Sandan Kasar Paris sun tabbatar da cewa kashi 60 (60%) na kiran wayar da Police Rescue suke amsawa da dare na mata ne da suke Neman agaji akan mazajen su.

French Secretary of State, Michelle Andrea ta fada lokacin da take Jawabi akan ‘Yancin Mata (Women’s Right) cewa: “Ko dabbobi a wasu lokutan ana yimasu Mu’amala mai kyau fiye da yadda ake yiwa mata, Saboda idan mutum ya daki kare (Dog) a titi wani zai iya zuwa yakai karar sa a Animal Care Society, amma idan mutum ya daki matar sa a titi baka ganin wani yace masa uffan, bare ma yakai karar sa gaban Kuliya.

•Dukan Mata a Kasar Ingila:- Kididdiga data fito daga Crime Survey for England and Wales ta tabbatar da cewa a Shekarar da ta gabata (2020) an doki mata kusan Miliyan daya da Dari Shida (1.6 Million).

Shehu Rahinat Na’Allah
4th October, 2021.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *