Fitaccen mawaki mai ƙaramin jiki na ƙasar Guinea, “Grand P” ya wallafa hotunansa da zuƙeƙiyar budurwarsa kuma rusheshiya mai suna “Eudoxie Yao”.

Soyayya dai wata abace wacce take zuwa idan jinin mutum biyu yahadu.

Tabbas, hakan batun yake idan akayi duba zuwa abin da ke faruwa tsakanin fitaccen mawaƙin nan dake ƙasar Guinea wanda aka fi sani da Grand P da kuma kantamemiyar budurwar sa wacce take yar asalin ƙasar Ivory Coast wato Eudoxie Yao.

Shi dai mawaƙin ya kasance yana da jiki dan ƙarami ne, amma ita budurwar danƙareriya ce, wanda hakan ya zama kamar wani abu na almara tsakanin mutanen guda biyu ma banbanta.

class="wp-block-image size-full">

To amma fa, ance so gamon jini ne, mawaƙin ya wallafa wasu hotuna shida wannan kantamemiyar budurwar tasa, masu kalamai dake daɗi kuma masu tausasa zuciya.

Waɗannan kalaman, tabbas, sun nuna yadda Grand P yake matuƙar ƙaunar sahibar sa.

A kalaman sa:

Ina son ki kasance cikin farin ciki a kowanne minti da dakika. Ina kaunar ki sosai kuma ina farin cikin kasancewar ki a rayuwa ta. Ina fatan ki cigaba da kasancewa mai samar min da farinciki ya abar kauna ta,” ya wallafa.

Ba don ni ba, saboda mutunci na, na rantse zan yi miki biyayya. Babu abinda zai sauya kauna ta gare ki. Ubangiji ya kare soyayyarmu. Eudoxie Yao,” ya ƙara da cewa.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *