Shine Shugaban Da Yafi Talauci A Nahiyar Afrika Na Shekarar 2021.

Shugaba Buhari Muhammadu na Najeriya harwayau a wannan shekarar ta 2021 shi ne shugaban da ya fi sauran takwarorinsa na nahiyar Afrika talauci.

Kamar yadda mujallar Forbes da Washington suka bayyana, cikin shekaru sama da shida da shugaban ya kwashe yana mulkar Najeriya adadin kuɗaɗen daya mallaka a lalitarsa shi ne Dala 150,000 wato kwatankwacin naira miliyan 30 , sannan sai gidaje 5 da kuma waɗansu gidaje biyu na ƙasa, ɗaya a mahaifarsa dake Daura sannan ɗaya a Katsina. Sai kuma garken shanu guda 270, tumakai 25 , dawakai 5 da kuma gonar noma.

Haƙiƙa duk da kasancewa shugaban yana da waɗansu kura-kurai a mulkinsa, amma ya sha bamban da shugabannin ƙasar na baya waɗanda suka wawure dukiyar ƙasar suka arzurta kawunansu da ƴaƴansu.

Daga Mutawakkil Gambo Doko.

One thought on “Shine Shugaban Da Yafi Talauci A Nahiyar Afrika Na Shekarar 2021.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *