ƘIDIDDIGA: Kawo yanzu Shugaba Buhari yayi tafiye-tafiye sau 130, yayinda kuma ya ziyarci ƙasashe daban-daban guda 36 tun bayan zamansa Shugaban Nigeria.

Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari yayi tafiye-tafiye sau 130 tare da ziyartar ƙasashen daban-daban har 36 a faɗin Duniya.

Ziyararsa ta ƙarshe zuwa wara shine zuwansa Dubai a farkon watan Dasamba inda ya samu rakiyar Ministoci har guda goma.

Masu kula da al’amuran yau da kullum suna ganin cewa waɗannan tafiye-tafiyen da Shugaba Buhari yayi ba su da amfani ɗari bisa ɗari ga al’amuran da suka shafi siyasa, tsaro da tattalin arziƙin Nigeria.

Daga | Ya’u Sule Tariwa

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *