Ƙungiyar Boko Haram ta yi garkuwa da mutane huɗu, kuma har kawo yanzu ba’a san makomar mutanen ba.

Daga | Ya’u Sule Tariwa,

Ƙungiyar Boko Haram ta wallafa sabon faifan Bidiyo wanda ya bayyana cewa sunyi garkuwa da mutane huɗu daga wurare daban-daban a Nigeria.

A cikin wani ɗan gajeren bidiyon da yake yawo a shafukan sada zumunta, an gano ɗaya daga cikin waɗanda abin ya ritsa da su mai suna Zakaria Azirkime ya bayyana irin halin da suke ciki.

Ya ce, “shi ma’aikacin ƙungiyar kula da walwalar ƙananan yara ne ta UNICEF, kuma sun ɗauke shi ne a hanyar Maiduguri zuwa Damboa.

Biyu daga ciki sun bayyana cewa an sace su ne daga yankin ƙauyen Buratai zuwa Buni Yadi na huɗun kuma wanda ma’aikacin kula da tafiye-tafiye (FRSC) ne, ya bayyana cewa yana hanyar zuwa Maiduguri daga Kano ne suka ɗauke shi.

Har’ilayau,

ƴan ta’addan na Boko Haram haryanzu basu nemi Gwamnati ko Iyalan waɗanda al’amarin ya shafa akan su bayarda kuɗin fansa kamar yadda suka sabayi idan sunyi garkuwa da mutane a baya ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *