Ƴan ƙabilar IGBO masu rajin kafa ƙasar Biafra sun kashe direban motar Dangote mai suna Saidu Alhassan da yaran aikinsa 2 a Jihar Imo.

Daga | Ya’u Sule Tariwa

Rahotanni sun tabbatarda cewa wasu da ake zargin ƴan ƙabilar IGBO ne sun kashe direban motar Ɗangote mai suna Saidu Alhassan tare da yaransa guda biyu, Halliru Mallam da Danjuma Isari a yankin ƙaramar hukumar Orsu ta Jihar Imo.

Al’amarin ya faru ne tun ranar Laraba a yayinda suke kan hanyarsu ta komawa Obajana bayan sauke buhunan siminti wanda daga nan ne fusatattun ƴan kabilar ta IGBO suka afka musu.

Rahotannin sun ƙara da cewa, ƴan ƙabilar ta IGBO sun tare su tare da umarnin kowannensu ya fito daga motar bayan fahimtar cewa dukkaninsu daga yankin Arewa suke, daga bisani kuma suka kashe su.

A

watan Afrilu ma sun kashe tsohon mai baiwa Atiku shawara wato Ahmed Gulak, duk a yunkurin neman ƴancin kafa ƙasar Biafra.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *