Ƴan bindiga sun kashe ɗalibi tare da garkuwa da wasu malamai a makarantar Nuhu Bamalli Polytechnic

Ƴan Bindiga Sun Kashe Ɗalibi Tare Da Garkuwa Da Wasu Laccarori A Makarantar Nuhu Bamalli Polytechnic

A daren ranar Alhamis, wasu gungun ƴan bindiga suka kai hari a makarantar Nuhu Maballi Polytechnic da ke Zaria, a yayin da suka harbi da garkuwa wasu ma’aikatan makarantar da ɗalibai. An tabbatar da Mutum ɗaya ya rasa ransa a sakamakon harbin.

Sakataren ƙungiyar ASUP, Aliyu Kofa ya tabbatar da ƴan bindigar sun hallaka ɗalibi ɗaya sannan sun yi garkuwa da malamai biyu.
Aliyu Kofa ya bayyana sunayen malaman da aka yi garkuwa da su kamar haka: Habila Nasai da kuma Malam Adamu Shika.

Sannan sanarwar, ta bayyana matar ɗaya daga cikin ma’aikatan makarantar, Ahmed Abdu da ƴaƴansa guda biyu da aka yi garkuwa da su, amm an sake su a safiyar ranar juma’a. Saidai bai yi ƙarin haske ba akan yadda aka yi suka kuɓuta.
Sannan ɗalibai guda biyu sun samu munanan raunuka sakamakon harbinsu da ƴan bindigar su ka yi musu.

“Ɗaya daga cikinsu sunan Ahmed, shi ne ya mutu a asibiti sakamakon raunikan daya samu, sauran kuma suna samun kulawa ta musamman a asibitin makaranta”, in ji Aliyu Kofa.

Jaridar PREMIUM TIMES ta tattauna da ɗaya daga cikin ma’aikatan makarantar a safiyar juma’a, a inda ya bayyana cewar an fara harbe-haren ne a tsakiyar dare a ranar Alhamis
“Ni da iyalina bama cikin harabar makaranta al’amarin ya faru, saboda tun a watan Nuwamba mu ka bar kwana a cikinta, amma na samu kira daga makwobtanmu da su ke cikin harabar makarantar a daren jiya, su ka sanar dani ana harbe-harbe a cikin harabar makarantar. Za ma ka iya jiyo sautin harbin bindiga daga wayar, tabbas wannan abin taƙaici ne”.

Daga Mutawakkil Gambo Doko

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *