Aƙalla mutane 23 aka kashe a Jos, yayinda suke bisa hanyar komawa gida daga wurin Maulidi wanda ya gudana a Bauchi.

Rahotanni sun tabbatarda kashe wasu matafiya 23 a yankin Rukuba na ƙaramar hukumar Jos ta Arewa, a Jihar Filato.

Harin ta’addancin wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane 23 tare da jikkata waɗansu ya faru ne da misalin ƙarfe 10:00am a safiyar yau Asabar.

Rahotannin sun kuma tabbatarda cewa al’amarin ya afku ne a yayinda matafiyan suke kan hanyarsu ta komawa gida Jihar Ondo, bayan halartar taron Maulidi wanda Sheikh Dahiru Bauchi ya gudanar a garin Bauchi.

Har’ilayau; ɗaya daga cikin waɗanda suka auna arziƙi, ya tabbatarda cewa aƙalla mutane 50 sun rankaya cikin dazuka domin tsira da rayukans.

Rahoto

| Ya’u Sule Tariwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *