Allah ɗaya gari bam-bam: A ƙasashen da su ka ci gaba sosai, kuɗin gyaran ƙananan amfani a gida ya fi sayen sabo tsada — Ja’afar Ja’afar

Jaafar Jaafar

Haƙiƙa Allah yayi mutane iri iri, kuma da salon rayuwa daban daban.

Hakan, yasa rayuwar ta banbanta, ta yadda idan wani abu ya faru sai yabaka mamaki, dariya da kuma tausayi a wani yanayin kuma sai dai kayi gum saboda tsabagen kiɗima.

Ja’afar Ja’afar fitaccen ƙwararren ɗan jarida ne da yake zaune a ƙasar Ingila.

Ya wallafa wani rubuta a shafin sa na kafar sadarwa ta Facebook, inda ya nuna mamakin sa akan yadda rayuwar ƙasashen da suka ci gaba take, da yadda suke fitar da kaya daga gida a wani salo na “Duk mai so ya ɗauka”.

class="has-text-align-justify">A cewar sa:

“Wasu suna da dama, wasu kuma basu da dama ta aljihu.”Wani ne ya fitar da wadannan abubuwa ya lika takarda cewa mai bukata ya dauka.

“Na dauki hoto na farko yau da rana. Na yi zaton idan na dawo zan ga wani ya dauka, to amma ga shi har dare ya yi babu wanda ya kula. Takardar ce kawai iska ta dauka.

Ja’afar Ja’afar

Ja’afar Ja’afar ya ƙara da cewa:

“Kwanaki talabijin mai shamulallen ‘sikirin’ na gani mai ita ya fitar a kofar gidansa duk mai so ya dauka, saboda watakil ya sayi sabuwa. Wannan talabijin din kanta ta yi kwanaki kafin mai bukata, ko masu kwashe shara su dauka.

“Ba a fi wata ba, firji da keken hawa na gani an fito da su ana neman mai so. Duk da a cikin rubutun daya wallafa yaci gaba da cewa:”Abin mamakin shi ne, akasarin wadan nan abubuwa su na aiki kalau, wasu kuma ‘fiyus’ ne watakil ya tsinke, amma ba za su gyara ba sai dai su sayi sabo.

A ƙasashen da su ka ci gaba sosai, kudin gyaran kananan abubawan gida ya fi sayen sabo tsada.” Inji Jaafar.

Hakan na zuwa ne a inda wasu ke neman irin kaya irin waɗannan ruwa a jallo da kuɗi zasu siya a ƙasashen mu, to amma sai gashi a wasu wuraren neman kai ake dasu.Haƙiƙa Allah daya gari bambam.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru.

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *