An kama wani tsoho ɗan shekara 70 dumu-dumu yana lalata da yarinya ƴar shekara 7 a Jihar Bauchi.

Daga | Ya’u Sule Tariwa

Rahotanni sun bayyana yadda aka kama wani tsoho ɗan shekara 70 mai suna Alhaji Umaru Daura yana lalata da yarinya ƴar shekara 7 a Jihar Bauchi.

Wannan rahoto yana ƙunshe cikin wani bayani da Jami’in hulda da Jama’a na rundunar ƴan Sanda, mai suna Thomas Goni ya miƙawa manema labarai yau Talata a Jihar Bauchi.

Mista Goni, ya bayyana cewa “al’amarin ya faru ne a ƙauyen Kawo Rauta dake ƙaramar hukumar Toro ta Jihar Bauchi”.

Ya

kuma ƙara da cewa “tun da farko dai mahaifin yarinyar mai shekaru 7 a Duniya mai suna Alhai Habu shine yayi ƙara zuwa ofishin ƴan Sanda, inda ya shaida cewa ƙiri-ƙiri aka kama tsohon yana cin zarafin yarinyar tasa.

A ƙarshe, Mista Goni ya bayyana cewa babban Sufeton ƴan Sanda sashi na 12, AIG Audu A. Madaki ya umarci a miƙa wannan dattijo gaban kotu domin ya girbi abinda ya shuka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *