Batun Kwamishe Naira Biliyan 19: Muna jajantawa Hukumar EFCC bisa labaran karya da yaudarar ‘yan Najeriya – Gwamnatin jihar Kogi.

Gwamnatin Jihar Kogi ta bayyana yunkurin Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati EFCC a matsayin abin dariya da yin katsalandan a cikin wani mummunan lamari da wata barna da nufin sake yaudarar ‘yan Najeriya.

A ranar Juma’ar da ta gabata ne Hukumar EFCC ta ce ta dawo da N19,333,333,333 da ake zargin ta kwato daga asusun ceto albashin Kogi wanda aka boye a bankin Sterling.

Sai dai a wata sanarwa mai taken ‘kurin da hukumar EFCC ke yi’, kwamishinan yada labarai da sadarwa na jihar Kogi, Kingsley Fanwo, ya ce gwamnati za ta shirya cikakken martani dangane da sabon matakin da hukumar ta dauka na cin fuskarta bisa la’akari da rashin sani da rashin da’a a cikin lamarin da ake jayayya.

“Sanarwar

da hukumar ta fitar, wani mummunan yunkuri ne na yi wa jihar zagon kasa kan lamarin da ba shi da alaka da jiharmu abar kauna,” inji shi.

“Muna tabbatar da gaskiyar cewa gwamnatin jihar Kogi ba ta gudanar da irin wannan asusu a bankin kamar yadda wata wasika da bankin ya rubuta. Muna jajanta wa hukumar EFCC domin ya kasance ta bayar da labarin karya da yaudara da gangan,” in ji sanarwar.

Fanwo ya jaddada cewa gwamnatin jihar Kogi za ta mayar da martani ga sabuwar sanarwar ta EFCC gaba daya, yana mai cewa “duk wani matakin da ya dace za mu bi shi don tabbatar da rashin gaskiya EFCC da kuma gaskiyar gwamnatinmu.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *