BIKIN SALLAH: Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi ya raba goron sallah ga al’ummar Musulmi mazauna Jihar Enugu.

Gwamnan Jihar Enugu, Ifeanyi Ugwuanyi ya bayarda kyautar kayayyakin abinci da wasu makuɗen kuɗaɗe da ba’a san adadinsu ba ga al’ummar Musulmi mazauna Jihar Enugu a matsayin goron sallah.

Kayayyakin sun haɗa da buhunan shinkafa, kayan marmari da manyan shanu guda biyu. Gwamnan ya bayarda wannan kyauta ne sa’o’i kaɗan da suka gabata, ta hannun Kwamishinan ayyuka, Mrs Mabel Agbo a babban Masallacin Enugu, tareda miƙa saƙon taya murna ga Musulmi musamman a yayinda suke tsaka da shugulgulan bikin sallah.

A gefe guda kuma, Sarkin Hausawan Jihar Enugu, mai suna Alhaji Abubakar Yusuf Sambo yayi farin ciki tare da miƙa godiya ga Gwamna Ugwuanyi bisa abin alkhairin da yayi wa al’ummar Musulmin da suke zaune a Jihar ta Enugu.

Rahoto | Ya’u Sule Tariwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *