Direba ya kashe jami’in Karota Kano.

Wani direba mai gudu ya kashe wani ma’aikacin hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta Kano, KAROTA, a kan titin BUK a cikin birnin Kano.

Sai dai kuma kokarin kama Direban ya ci tura, domin kuwa ya gudu bayan ya buge ma’aikacin.

Kakakin hukumar KAROTA, Nabilusi Bako ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an kai gawar jami’in asibitin Murtala Muhammad dake birnin Kano.

Mista Bako ya ce ba zai iya yin karin bayani kan lamarin ba yayin da hukumar ke jiran rahoto daga asibitin.

Daga nan ya yi alkawarin bayar da cikakken bayani bayan bincike.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *