Gwamna Zulum ya raba Naira miliyan 84 ga ƴan gudun hijirar da suka koma gidajensu a yankin Bama, Jihar Borno.

Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum ya raba naira miliyan 84 ga mutanen da suka dawo gidajensu daga gudun hijira a ƙauyen Banki dake ƙaramar hukumar Bama ta Jihar Borno.

Ɗaruruwan ƴan gudun hijara sun koma gidajensu daga Nijar da Kamaru sakamakon rikicin Boko Haram da yayi ƙamari a yankunan.

Har’ilayau; wannan yana ƙunshe cikin jawabin da mataimakin Gwamna Zulum mai suna Isa Gusau ya bayyana a yau Juma’a.

A ƙarshe, Kamfanin dillancin labarai na NAN ya rawaito cewa kowanne magidanci ya rabauta da tallafin aƙalla naira dubu 40.

Rahoto

| Ya’u Sule Tariwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *