Ina da yaƙinin nasara a ƙoƙarinmu na fitar da ƴan Nigeria miliyan 100 daga talauci. ~Inji Shugaba Buhari

Shugaba Buhari ya bayyana cewa yana da yaƙinin Gwamnatinsa zata cimma ƙudirin fitarda ƴan Nigeria miliyan 100 daga talauci.

Shugaban ya bayyana haka ne a safiyar yau Juma’a, loƙacin da yake miƙa saƙo na musamman ga ƴan Nigeria dai-dai loƙacin da ƙasar take murnar cika shekaru 61 da samun yancin-kai.

Buhari ya ce, fitar da ƴan Nigeria mutum miliyan ɗari al’amari ne mai sauƙi, bisa la’akarin yadda tsarukan da Gwamnati take bijirowa da su suke ƙara samun tagomashi. Domin a halin yanzu masu cin gajiyar shirin N-Power sun tashi daga mutane dubu 500,000 sun zama miliyan 1,000,000 a faɗin Nigeria.

Hakazalika,

a halin yanzu shirin Gwamnatin tarayya na ciyar da ɗalibai ya karaɗe Jihohi 36. Mata dubu 103,000 aka ɗauka a matsayin masu daukar nauyin kula da dafa abincin, yayinda ɗaliban Firamare aƙalla miliyan goma ne suke amfana da wannan tsari a faɗin Nigeria.

A ƙarshe Shugaba Buhari ya bayyana cewa “ya sake bayarda umarni domin faɗaɗa shirin bayarda rance ga manoma domin haɓɓaka harkokin noma da kiwo a faɗin Nigeria. Waɗannan sune hanyoyi da muke amfani kuma daga nan zuwa wani loƙaci za’a rage raɗaɗin talauci a Nigeria.

Rahoto | Ya’u Sule Tariwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *