Ina gad da dawowa harkar film- in ji tsohuwar jarumar fina-finan Hausa Maryam Abubakar Jan Kunne

Ina Gab Da Dawowa Harkar Film- Maryam Abubakar Jan Kunne

Tsohuwar fitacciyar jarumar fina-finan Hausa Maryam Abubakar ta bayyana cewa tana gad da dawowa harkar film.

Maryam Abubakar wacce aka fi sani da Maryam Jan Kunne ta bayyana hakan ne a cikin wata hira ta musanman da ta yi da sashen Hausa na BBC.

“Eh ina da burin komawa harkar film, amma gaskiya ba kowanne film zan yi ba sai wanda zai faɗakar da al’umma, amma idan aka kawo mini labarin film na karanta na ga shirme ne gaskiya ba zan yi ba”

Jaruma Maryam Abubakar Jan Kunne ta yi fina-finai da yawa musamman tare da tsohon saurayinta Sani Danja irinsu: Jan Kunne, Adamsi, Jarumai da sauransu

Daga: Mutawakkil Gambo Doko

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *