Jean-Pierre Adams ya kwashe shekaru 39 a sume ba tare daya farka ba

Adams shine mutumin da yayi sheku 39 a sume, kuma har yanzu yana nan da ransa.

Jean-Pierre Adams ya kasance a sume tun shekaru 39 da suka wuce.

Labarin tsohon tauraron kwallon kafa Jean-Pierre Adams na daya daga cikin labaran ban mamaki.

Tsohon dan kwallon na kasar Faransa ya tafi asibiti ne don ayi masa tiyata a gwiwarsa a shekara ta 1982, kuma tun daga wannan lokacin ya shiga halin ha’ula’i.

An haife shi a kasar Senegal, Adams ya koma Faransa tun yana dan shekara 10, kuma ya yi wasa a kungiyoyin Faransa da dama da suka hada da Nice da Paris Saint-Germain.

Adams wanda ake yiwa lakabi da “The Black Rock”, ya kuma bugawa kasar Faransa wasanni 22 a tsakanin 1972 da 1976.

Amma rayuwarsa ta ɗauki mummunan yanayi shekara ɗaya bayan ya yi ritaya a shekara, lokacin da aka yi masa rajista zuwa asibitin Nice don ayi masa tiyata a gyara masa jijiyar sa da ta fashe.

An bawa Adams wani magani na wanda zai yi barci kafin a fara aikin, sai dai kuma maganin ya jefashi zuwa dogon suma.

Matashin mai shekaru 34 ya sha wahalar bugun iska, wanda ya addabi kwakwalwarsa da iskar oxygen.

Har yanzu yana cikin suma, har zuwa yau da yake da shekara 73 a Duniya.

Matar Adams ta kasance a tare da shi bayan duk waɗannan shekarun.

Tsawon shekaru 39, matar Adams Bernadette ta kasance tare da shi.

A cewar Bernadette, mijinta na iya numfashi, yana cin abinci, kuma yana yin tari shi kadai ba tare da bukatar taimakon kayan aikin likita ba.

“Kawai ba ni da karfin gwiwar daina ba shi abinci da ruwa.

“Yana da ayyukan yau da kullun. Yana farkawa da ƙarfe 7, yana cin abinci… Mai yiwuwa yana cikin yanayin fita daga hayyaci, amma yana iya ji da zama a cikin keke.

Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta PSG Jean-Pierre Adams ya kasance cikin rashin lafiya tsawon shekaru 39 bayan ya sha maganin na sa kai wanda hakan zai hana shi fita na wasu ‘yan awanni. Ya ji rauni a gwiwa a ranar 17 ga Maris, 1982.

Dan wasan har yanzu yana cikin suma har zuwa yau, yana da shekara 73.

Kundin adana abubuwan tarihi na duniya wato Guinness World Records ya karrama shi a matsayin mutumin daya fi daɗewa a sume a tarihin duniya.

Daga Mutawakkil Gambo Doko

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *