Kisan mutane 42 da ƴan bindiga suka yi ta hanyar ƙone matafiya a Sokoto yana cigaba da ɗaga hankulan al’ummar Nigeria.

A jiya ne ƴan bindiga suka ƙone matafiya 42 yayin da suke hanyar zuwa garin Issa, daga Sabon Birni.

Waɗanda al’amarin ya rutsa da su sun haɗa da maza, mata da ƙananan yara. Rahotanni sun kuma tabbatarda cewa mutane aƙalla uku daga ciki sun tsira da ransu yayinda suke Asibiti karbar magani.

Anyi jana’izar matafiyan ne a yammacin Jiya Talata.

Daga

| Ya’u Sule Tariwa

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *