Ko akwai sunan Gidan rediyo ne a Lokacin Annabi s.a.w, da har ‘yan Jarida suke Rahoto? ‘Dan Jarida Ja’afar Ja’afar ya tambayi Sheikh daurawa.

Wani jawabi da babban malamin nan da ke Kano, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, ya yi a yayin hudubar Juma’a na cewa mafi yawan fitintunu a zamanin Annabi Muhammad (saw) yan jarida ne suka hada ya janyo cece-kuce a shafukan sada zumunta.

A jawabin da malamin ya yi da ake yadawa a faifan bidiyo, ya bayyana cewa da yawan fitintunu da yake-yaken da aka yi a tarihin duniya yan jarida ne suka hada.

“Duk

fitinar duniya yan jarida ne suka hadata. Duk tashin hankalin duniya yan jarida ne suka hadashi,” a cewar malamin.

Ya kuma kara da cewa ko a zamanin Manzon Allah yan jarida sun taka muhimmiyar rawa wajen tayar da zaune tsaye.

“Tun zamanin Annabi yan jarida kaso 75 cikin 100 su ne munafukan da suke lalata addini,” cewar Daurawa.

Sai dai kuma ba a kyale malamin haka ba. Tuni yan jarida suka fara bayyana ra’ayoyinsu akan malamin inda suka zubo masa ruwan tambayoyi masu caja kwakwalwa.

Babban dan jaridar nan dan asalin jihar Kano da ya bankado bidiyoyin da suke nuna Gwamna Ganduje yana zuba dalolili a aljihun babbar riga, Ja’afar Ja’afar, ya tambayi ko akwai wani gidan rediyo ne a zamanin Annabi da har yan jarida suke rahoto.

“Ya sunan gidajen rediyon lokacin? Na san dai sai an yi daram, akan yi kwandi,” dan jaridar ya tambaya.

Shi kam matashin marubucin nan a shafukan sada-zumunta wato Aliyu Dahiru, cewa ya yi ai ba yau malamin ya saba zubo zance babu lissafi ba. A cewarsa a baya ma ya taba cewa Allah ya yi kunar bakin wake.

“Shi Daurawa ba ya sakawa bakinsa linzami wallahi. Haka ma fa ana zaune kalau ya ce wai Allah ya taba yin kunar bakin wake. Yanzu kuma ya ce wai yan jarida ne suka dinga hada rigima a zamanin Annabi,” cewar matashin.

Mun nemi jin ta bakin shehin malamin domin ya yi karin bayani akan furucin nasa amma abin ya ci tura a yayin da maganar tasa ta dauki zafi a shafin Facebook.

Daga: Habibu Wali

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *