Ku cigaba da haƙuri, a yayinda muke ta ƙoƙarin shawo kan matsalolin da ƙasa ke ciki. | ~Shugaba Buhari ya faɗawa ƴan Nigeria

Yayin aikewa da saƙon barka da Sallah ga ɗaukacin Musulmi, Shugaba Muhammadu Buhari ya alaƙanta ƙalubalen da Nigeria take fuskanta da ɓullar annobar Korona.

Kamar yadda bayanai suka fito daga shafin mai magana da yawun Shugaban ƙasa, wato Garba Shehu; Buhari ya jaddada irin ƙoƙarin da Gwamnatinsa take wajen samarda cigaba da walwala ga ɗaukacin al’ummar Nigeria.

Shugaba Buhari ya bayyana cewa, “duk da asarar da aka samu wanda ambaliyar ruwa ya janyo a wasu yankunan”, har kawo yanzu Gwabnatinmu baza ta laminci yunƙurin wasu ƴan Kasuwa na shigo da shinkafa ta ɓarauniyar hanya ba, domin hakan shi yake sanya manoman cikin gida suke sayar da kayan noman su cikin farashi mai araha.

A ƙarshe; Buhari ya bayyana cewa, “a matsayi na na zaɓaɓɓen Shugaban ƙasa, wanda ya samu dukkan goyon bayan al’ummar ƙasa, “Ina tabbatarda cewa muna cigaba da ɗaukar matakai domin sauƙaƙa rayuwa ga al’immar Nigeria, ciki harda samarda tsaro da takin zamani domin wadatuwar manoman karkara.

Ratoho | Ya’u Sule Tariwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *