Ku kare kanku idan ƴan bindiga su ka kai muku farmaki- in ji gwamna Matawalle

Ku Kare Kanku Idan Ƴan Bindiga Suka Kai Muku Farmaki- In Ji Matawalle

Gwamnatin jihar Zamfata ta soke bikin ranar demokaraɗiya na wannan shekarar saboda taɓarɓaren tsaro a jihar.
Sannan ta umarci al’ummar jihar da su kare kanku daga mafarkin ƴan ta’adda.
Gwamna Bello Matawalle ya yi wannan kiran ne a yau a loƙacin gudanar da addu’o’in da gwamnati ta shirya akan samun kariya daga hare-haren ƴan ta’adda
“Matsalar tsaro tana buƙatar a samu mafita, dan haka yakamata mutane su kare kansu”, in ji Matawalle
“Ina kiran mutanen jihar Zamfara da su kare kansu idan ƴan ta’adda su ka kai musu farmaki, gwamnatina ta baku dama idan ƴan bindiga suka kai muku farmaki kada ku jira sai jami’an tsaro sun kawo muku ɗauki, ku tashi ku kare kanku, kuma gwamnati ta shirya ɗaukar ma’aikatan sakai a cikin kowanne gari waɗanda za a ɗora musu alhakin kare ƙauyansu daga hare-haren ƴan ta’adda”
“Ina kuma kira ga sarakunan gargajiya da shugabannin al’umma su tabbatar mutanen da su ke da ƙima ne za a ɗauka a aikin sa kai”

Daga Mutawakkil Gambo Doko

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *