Mawaƙi Davido ya sadaukar da miliyan 200, wanda abokai da mabiyansa suka haɗa masa tare da ƙarin miliyan 50 zuwa ga gidajen marayu a faɗin Nigeria.

Daga | Ya’u Sule Tariwa,

Shahararren mawaƙin Nigeria mai suna David Adeleke wanda aka fi sani da Davido ya kyautar da miliyoyin kuɗaɗen da abokansa suka tara masa har miliyan ɗari biyu ga gidajen marayu a faɗin Nigeria.

Cikin wata takarda da aka wallafa ɗauke da sa hannun shahararren mawaƙin; Davido ya bayyana godiyarsa ga ɗumbin abokan sana’arsa da masoyansa waɗanda suka haɗa masa kuɗaɗen cikin sa’o’i 48.

Bayan haka ne kuma ya sake yin albishirin cewa shima ya sadaukar da kuɗaɗen ga gidajen marayu a faɗin Nigeria, tare da karin miliyan hamsin daga aljihunsa, wanda jumulla kuɗaɗen suka zama miliyan ɗari biyu da hamsin kenan.

Ya

kuma kafa Kwamiti wanda ya ƙunshi mutane biyar, tare da miƙa musu ragamar raba kuɗaɗen zuwa gidajen marayun dake a Jihohi 36 harda babban birnin tarayya Abuja.

A ƙarshe, Davido ya bayyana cewa bashi da buri face yaga ya taimakawa marasa ƙarfi da marayu; a gefe guda kuma ya bayyana alfaharinsa bisa ga irin abinda abokai da mabiyansa suka yi masa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *