Rahama hassan tace Arewa tamu ce

Tsohuwar jaruma Rahama Hasan tace …Assalamu Alaikum

AREWA TA MUCE DUKA

A kwana biyunnan yawancin Post din da yafi yawa duk akan Arewa ne, kowa yana daura laifi kan Shugabanni.

To musani Kowa dan Arewa ne cikinmu kuma yana da gudumawar da zai bayar wajen gina Arewa,

Yan Uwana idan har Muna jira Yan Majalisu da Sanatoci ko masu rike da mukami na siyasa ne zasu gyara mana Arewa su kadai to hakika mun yaudari kanmu.

Domin tun Asali basu je wajen da niyar haka ba, bayan haka kuma abun ya musu yawa bazasu iya su kadai ba dole sai mun tallafa musu da iya abinda zamu iya

Duk

Al’umman da suke son gina kansu basu dogara kan wasu kadan a cikinsu dole ne kowa yasan abinda yake kansa ya aiwatar ta hanyar da ta dace tofa anan ne zamuga irin cigaban da mukeso .

Dole ne ko wannenmu yayi kishin Arewa a Aikace bawai da surutu ba,

A yau idan kasan mutuncin dattawan Unguwanku ka iya bayar da gudumawa a cikin Unguwar da duk irin daman da kake dashi, kama daga tsaro, tsafta, taimakon wanda kafi karfi, shiga gayya a duk wani aikin da Unguwan take bukata, sannan kaso kowa da Alkhairi, kayi kokarin shigo da duk wani abinda kasan zai taimaki Unguwanku, to hakika ka taimaki Arewa kuma ka gina Arewa ba tare da kajira wata gwamnati ba, kowa yasan mai zai iya,

Sannan Mu yawai zikirori da Salati wa Annabi da Istgfari don Gyaran zukatanmu wanda ta cikia da Hassada da Bakin ciki da keta da mugunta.

Ta irin wadannan hanyoyi ne kawai nake ganin Arewa zata gino amma in ba haka ba sai dai kullum muyi ta ihu an kwace mana hakkinmu al hali kuma babu wanda ya kwace mune mukaki bin hanyar da zamu isa gareshi cikin sauki

Allah hada kan Al’ummarmu ya bamu zaman lafiya yasa mu iya tashi mu gyara.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *