Sakamakon rahoto mai karfafa gwiwa na zaman lafiya da muka samu a lunguna da sako na jihar Zamfara, mun saki layikan waya a yankunan da muka katse – Cewar Gwamna Matawalle.

Gwamnan jihar Zamfara, Bello Matawalle, ya sanar da dakatar da dokar hana ayyukan sadarwa a jihar.

Ya bayyana hakan ne a ranar Asabar a wani taron da aka gudanar a Gusau, babban birnin jihar, inda ya bayyana cewa za a fara aikin sadarwa a ranar Litinin mai zuwa.

“Ina so in sanar a yau (Asabar) cewa mun dauki matakin dage takunkumin hana sadarwa a jihar,” kamar yadda gwamnan ya ruwaito a cikin wata sanarwa da Zailani Bappa, mai ba shi shawara na musamman kan wayar da kan jama’a, da harkokin yada labarai, ya fitar. .

“Insha

Allahu, daga ranar litinin mai zuwa.”

Ya bayyana cewa an sanar da matakin dakatar da matakin ne sakamakon wani rahoto mai karfafa gwiwa na zaman lafiya da aka samu a lunguna da sako na jihar.

Gwamna Matawalle, wanda ya bayyana hakan a wajen taron jam’iyyar APC reshen jihar da aka gudanar a harabar baje kolin kasuwanci da ke Gusau, ya yi imanin cewa ‘yan bindiga sun fahimci abin da ake bukata da matakin.

Ya godewa al’ummar jihar bisa hakuri da juriya da suka nuna a tsawon lokacin aikin, ya kuma ba su tabbacin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da daukar duk wani mataki da ya dace don wanzar da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyinsu.

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *