Shugaba Buhari ya samu nasarar ƙwato sama da tiriliyan ɗaya a hannun ɓarayin Gwamnati cikin shekaru shida. ~Jam’iyyar APC

Wani ɓangaren yaƙin neman zaɓe a Jami’iyyar APC ya bayyana cewa aƙalla nera tiriliyan ɗaya Shugaba Buhari ya ƙwato a hannun ɓarayin Gwamnati cikin shekaru shida.

Ɓangaren mai taken “Legacy Awareness and Campaign” a turance ya bayyana wannan ne yau Juma’a yayin wani taro da ya gudana a babban birnin tarayya Abuja. Kuma Gwamnatin Buhari ta karkata ne wajen ƙwato dukoyin al’umma da wasu tsirari su ka wawashe.

Ɗaya daga cikin ƙoƙarin Buhari shine, “na kirkirar Kwamitin masu bayarda shawara gameda ayyukan cin-hanci da rashawa (PACAC) wanda hakan ya taimaka wajen samun nasarar ƙwato kuɗaɗen da ɓarayi suka handame.”

Kamar

yadda Jaridar Vanguard ta wallafa; Ƙungiyar ta bayyana yadda aka ƙwato maƙudan kuɗaɗen, ciki har dala-miliyan $322 da ake zargin tsohon Shugaba Sani Abacha ya wawure.

A ƙarshe, wannan ƙungiya ta bayyana gamsuwarta bisa yadda Gwamnatin Buhari ta mayarda hankali wajen haraji da kuma bayarda rance ga manoma wanda ta hakan ne talakawa su ke samun damar dogara da kansu.

Rahoto | Ya’u Sule Tariwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *