Tababbun mayaƙan ƙungiyar Boko Haram sun yi zanga-zanga tare da farfasa abubuwa akan Gwamnati ta sallame su daga sansanin da ake tsare da su domin zuwa su gana da iyalansu.

Daga | Ya’u Sule Tariwa,

Tsofaffin mayaƙan Boko Haram waɗanda suka miƙa wuya tare da zubar da makaman yaƙi a baya sun fara zanga-zanga a wuraren da aka ajiye su.

Zanga-zangar kamar yadda rahotanni suka tabbatar shine karo na huɗu, kuma babban muƙasudinta shine suna cewa sun gaji da zaman sansanonin da ake tsare da su.

Kamar yadda wasu bayanai suka fito daga Jami’an tsaro masu kula da sansanin da ake tsare da tubabbun ƴan Boko Haram ɗin; Jami’an sun bayyana cewa ba komai ya janyo zanga-zangar ta tsofaffin mayaƙan na Boko Haram ba, face sai kiransu ga Gwamnati akan ta sallame su ko kuma tasan inda zata yi da su, a cewarsu sun gaji da zaman sansanin.

Sun

ƙara da cewa, an ajiye su a sansanonin sama da watanni huɗu ba tare da ganin iyalansu ba. Daɗin daɗawa yayin zanga-zangar an tabbatar da tsoffin mayaƙan na Boko Haram sun farfasa waɗansu abubuwa dake a sansanin na garin Maiduguri, Jihar Borno.

Kuma an bayyana cewa, tun a baya waɗansu daga ciki tubabbun mayaƙan na Boko Haram suka tsere ta ɓarauniyar hanya domin sun gaji da zaman sansanin nasu.

One thought on “Tababbun mayaƙan ƙungiyar Boko Haram sun yi zanga-zanga tare da farfasa abubuwa akan Gwamnati ta sallame su daga sansanin da ake tsare da su domin zuwa su gana da iyalansu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *