Tabbas ni na kashe mijina ta hanyar daba masa wuka, Rumasa’u Muhammed ta fadawa kotun Yolan jihar Adamawa.

Wata yarinya ‘yar shekara 19 da ake zargi da dabawa mijinta wuka ta amince da yin hakan.

Matashiyar, Rumasa’u Muhammed, ta amince ta dabawa mijinta, Mohammed Adamu dan shekara 35 wuka har sai da ya mutu.

An gurfanar da ita a gaban babbar kotun majistare ta Yola 1, yarinyar ta amsa laifin kisan kai.

Rumasa’u, wadda ta fito daga Wuro Yanka da ke karamar hukumar Shelleng a Yola, ‘yan sanda sun damketa da laifin kashe mijinta bayan ya ki amsa bukatar ta na sakin ta.

Ma’auratan

sun yi zama na ɗan gajeren lokaci, kasancewar ba da son ranta ba aka aura mata shi.

An bayar da rahoton cewa auren ya dauki makonni uku ne kacal kafin ta dauki alhakin kawo karshen sa.

An daura auren ne a ranar 6 ga watan Agusta, 2021, kuma bayan makonni uku mai aukuwa ta auku, bayan haka aka kama ta sannan aka gurfanar da ita a gaban kotu.

Rahoton Farko na (FIR) akan lamarin ya nuna cewa bayan wadda ake kara ta yiwa mijinta rauni da wuka a wata rana mai muni, mijin ya fadi, ya suma, daga baya aka tabbatar da mutuwarsa a asibitin da aka kai shi.

Lokacin da aka karanta abubuwan da ke cikin rahoton FI ga wadda ake tuhuma a kotu, ta yarda ta aikata laifin.

Daga nan sai mai gabatar da kara ya roki kotun da ta dage sauraren karar don baiwa ‘yan sanda damar mika fayil din karar zuwa ga Directorate of Public Prosecution domin samun shawara ta shari’a.

Alkalin Kotun Mai shari’a Aliyu Bawuro ya bayar da umarnin a tsare wadda ake kara a gidan yari sannan ya dage shari’ar zuwa ranar 13 ga Oktoba, 2021.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *