Wani mutum ya hallaka matarsa sakamakon ta hana shi rancen kuɗi ₦2,000.

Wani mutum mai shekaru 45 a Duniya, Mr Christopher ya lakaɗawa matarsa duka lamarin daya janyo mutuwarta sakamakon cece-kucen daya haɗa su akan rancen kuɗi naira dubu biyu 2,000 kacal.

Al’amarin ya faru ne ayau Lahadi cikin yankin Usulu dake Benin a Jihar Edo, sakamakon mijin ya tambayi matarsa mai suna Isoken Christopher rancen naira dubu biyu ita kuma ta hana shi, daga nan kuma ya hau dukan ta har sai da Rai yayi halinsa.

Ɗaya daga cikin iyalan mutumin da aka kama da wannan aika-aika ya bayyanawa manema labarai cewa ba wannan ne karon farko ba, a loƙuta da dama mahaifinsu yana cin zarafin mahaifiyarsu da gangan.

A

halin yanzu dai Mista Christopher yana hannun jami’an ƴan Sanda yayin da ake cigaba da binciken ƙwaƙwaf game da faruwar al’amarin.

Rahoto | Ya’u Sule Tariwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *