Wasu fusatattun matasa a garin Jos sun kwace gawarwakin mutanen da aka kashe daga Asibiti sun kaisu Ofishin Gwamna da Majalisar Dokokin Jihar.

Fusatattun matasan sun kutsa kai cikin Asibitin Specialist dake garin Jos a a yammacin yau Labara, inda suka shiga bangaren da aka ajiye gawarwakin mutanen da aka kashe suka kwashe su da karfin tsiya suka zuba su acikin mota.

Daga nan suka fara zarce wa Majalisar Dokokin Jihar don su nanawa ‘yan majalisun gawarwakin mutanen da aka hallaka.

Duk da Jawabin da Shugaban Majalisar yayi musu don su samu kwanciyar hankali, basu gamsu da Jawabin ba seda suka zarce har Ofishin Gwamnan Jihar kuma suka zube masa gawarwakin mutanen a kasa.

Zuwa

yanzu dai ba aji bayanan da suka fito daga bakin Gwamnan Jihar ba game da korafin da matasan suka gabatar masa.

Daga Kabiru Ado Muhd

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *