Wata Sabuwa: Ummi Zeezee ta roki Allah ya tsare ‘ya’yanta kada su zama ‘yan fim.

Tsohuwar jarumar masana’antar fina-finan hausa ta Kannywood Ummi Zeezee ta roki Allah idan ya bata ‘ya’ya kada suzama jaruman fina-fina.

Ummi Zeezee ta yi wannam addu’ar a shafinta na Instagram, inda ta wallafa addu’ar tata da turanci karamar haka:-

Ya Allah here is my prayer, when ever you get me “married “ and blessed me with children do not make them “Film Actors“.

Fassara:

Ya Allah ga addu’ata, duk lokacin da ka bani mijin “aure” kuma ka albarkace ni da ‘ya’ya kada ka sanya su zama “Yan wasan Fim”.

Ummi Zeezee ta kasance tsohuwar jaruma a masana’antar Kannywood, ta kasance jaruma mai tashe a lokacin da take haskawa a Fina-finan hausa, sai dai kuma a wannan lokacin Ummi Zeezee tana fuskantar tsananin rayuwa, wadda tasa har tayi ikirarin zata kashe kanta.

Ko me yasa Ummi Zeezee bata son ‘ya’yan da zata haifa su zamo taurari a harkar fim?

Wata kila hakan yana da nasaba da irin yadda rayuwa tajuyawa tsohuwar Jarumar baya a yanzu da tabar harkar, to koma dai menene, ita dai Ummi Zeezee ta yi tashenta a Kannywood ta gama, kuma dama haka al’amuran Kannywood suke, a lokacin da tauraruwar wata tadaina haskawa, a lokacin ne kuma ta wata zata fara haskawa.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *