Ya kamata ƴan Nigeria su ƙarawa Shugaba Buhari wa’adin shekaru huɗu ko biyar domin ya kammala ayyukan alkhairin da ya fara. ~Inji Mawaƙi Rarara

Shahararren mawaƙin siyasa mai suna Dauda Adamu Kahutu wanda aka fi sani da Rarara, ya bayyana sha’awarsa tare da shawartar ƴan Nigeria akan ya kamata su ƙarawa Shugaba Buhari shekaru huɗu ko biyar kafin ya sauka.

Mawaƙin ya bayyana haka ne cikin wani bidiyo mai tsawon daƙiƙa 50 wanda BBC Hausa suka yi fira da shi.

Rarara ya ƙara da cewa, Buhari ya ɗauko ayyukan alkhairi ga Nigeria, kuma idan da za’a bi ta ra’ayinsa sai “ya kamata a ƙarawa Shugaba Buhari wa’adin shekaru domin ya kammala gyaran Nigeria.

Rahoto

| Ya’u Sule Tariwa

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *