Yadda wani matashi ya aika kansa barzahu saboda shiga caca da ₦150,000 na kamfanin da yakewa aiki a Abuja.

Wani matashi mai ya kashe kansa bayan da ya yi asarar ₦150,000 a caca, can cikin wani gari waishi Pegi da ke ƙaramar hukumar Kuje a Abuja.

Matashin mai suna Adegbite, an ruwaito cewa ya yi caca ne da kuɗin da maigidansa ya ba shi ya biya abokan aikinsa, to amma abinka da mai neman na fura kawai sai Adegbite ya shiga caca da kuɗin da fatan ya maye gurbinsu bayan ya yi nasara.

Wani abokin aikinsa da ya zanta da Punch, ya ce Adegbite ya kashe kansa ne bayan ya yi asarar kuɗin kamfanin ta hanyar yin cacar wasanni.

class="wp-block-image size-full">

A cewar sa:

“Mun yi mamakin lokacin da abin ya faru. An ba shi kuɗin ya biya wasu mutane a wurin aiki. Kuɗaɗen sun kai kimanin ₦150,000. To amma kawai sai ya ɗauki kuɗin zuwa wani shagon yin caca ta ƙwallon ƙafa ya zuba. Sai Ya zaɓi wasu wasanni amma bai yi nasara ba.

“Washe gari, makwabta ba su gan shi ba. Sai suka lura yana ciki; suka fasa ƙofar suka tarar da jikinshi a sandare akan fankar sili yana lilo.Sai aka sanar da ƴan sanda, waɗanda suka ɗauke gawarsa,” inji abokin aikin.

Kakakin rundunar ƴan sandan babban birnin tarayya, DSP Josephine Adeh, ya tabbatar da faruwar lamarin, ya kuma ƙara da cewa ana ci gaba da gudanar da bincike akan lamarin.

Rahoto: Abubakar Mustapha Kiru

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *