‘Yar gidan sheikh Ibrahim El-zakzaky Suhaila ta shiga mawuyacin hali saboda cigaba da tsare iyayenta.

‘Yar Gidan Sheikh Ibrahim El-zakzaky, Suhaila El-zakzay Na cigaba da kukan rashin sakin Mahaifin ta da mahaifiyar ta wadanda suke ci gaba da zama tsare yanzu haka.

Suhaila ta bayyana cewa irin mawuyacin halin da take cigaba da shiga a ‘yan kwanakin nan akan tunanin iyayen ta ya yi muni sosai.

A don haka take kira ga Gwamnatin Jihar Kaduna da ta tarayya da su sakar mata iyayen ta.

Idan baku manta ba sheikh Ibrahim El-zakzaky da matarsa sun shafe shekaru a tsare a kurkuku tun bayan takaddamar da ta faru tsakanin ‘yan shi’a da tsohon Hafsan Sojin Najeriya Janar Tukur Burutai.

Tun a wancan lokacin kotu ta bada umarnin sakinsu, amma hukumomin Najeriya basu sake su ba.

A halin yanzu sheikh Ibrahim El-zakzaky yana fuskantar Shari’ar tsakaninsa da gwamnatin jihar Kaduna kan wasu tuhume-tuhume da gwamnatin take yimasa.

Shin kuna goyon bayan sakin iyayen Suhaila da gwamnati ke tsare dasu?

Daga Kabiru Ado Muhd

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *