WATA SABUWA: Shugaba Buhari ya amince da korar ma’aikatan Kwamfanin rarraba wutar lantarki, AEDC dake babban birnin tarayya Abuja.

Shugaba Muhammadu Buhari ya amince da korar ma’aikatan Kwanfanin rarraba wutar lantarki AEDC dake babban birnin tarayya Abuja.

Mai magana da yawun Ministan wutan lantarki mai suna Ofem Uket shine ya bayyana hakan yau Talata ga manema labaru.

A cewarsa, Buhari ya kuma amince da naɗa sabbin ma’aika na wucin gadi waɗanda zasu rinƙa gabatar da al’amura a Kwanfanin kafin zuwa wani ɗan loɗaci.

Matakin na Shugaban ƙasa dai ya tabbata ne biyo bayan zanga-zangar da ƙungiyar ma’aikata wutar Lantarki ta ƙasa suka gudanar a kwanakin baya tare da iƙirarin cewa ba’a biyansu albashi yadda ya kamata. Lamarin kuma da ya janyo rasa wutan lantarki na tsawon kwanaki a birnin tarayya Abuja da wasu sassan Jihohin Kogi, Nassarawa da Niger.

Daga

| Ya’u Sule Tariwa

Advertisements

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *