A duk nageriya gwamnonin PDP ne ka’dai ke Ayyukan alkhari amma Gwamnonin APC bacci kawai suke kwasa ~Cewar Atiku Abubakar.

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya bayyana cewa Jihohin da Jam’iyyar PDP ke iko da su ne kadai ke aikin Daya Kamata

Ya yi ikirarin cewa jihohin da jam’iyyar All Progressives Congress ke iko da su kawai suna barci ne saboda ba su wani aiwatar da ayyuka a can Jihohin nasu.

Atiku Abubakar ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kaddamar da titi mai tsawon kilomita 4.2 da gwamnatin jihar Bauchi ta gina, ranar Alhamis a Bauchi. Ya kuma yi kira ga gwamnatin tarayya da ta yi koyi da jahohin PDP.

Titin

Gombe zuwa Maiduguri mai suna: Titin Alhaji Atiku Abubakar.

Ya kuma yabawa gwamnan jihar Bauchi Bala Mohammed bisa irin nasarorin da ya samu a jihar cikin shekaru biyu da rabi yana mulki.

Atiku ya ce, “Bari in fara da yaba muku domin kun yi Aiki Mai kyau sosai. Tsawon sa’o’i kadan da na yi a Bauchi a yau, na yi sha’awar irin ci gaban da aka samu na samar da ababen more rayuwa da ni kaina na gani da Ido na ba tare da anbani labari ba.

“Wadannan tsare-tsare da kuka aiwatar da kuma ci gaba da aiwatarwa, su ne ginshikin ci gaba walau ta fuskar ilimi, kiwon lafiya ko duk wani abu na ci gaba. Amma, mafi mahimmanci, waɗannan ayyukan ci gaba sun zama tushen hanyoyin ƙarfafa tattalin arziki.

Ta hanyar ƙarfafa tattalin arziƙi, sun kuma samar da dubban ayyukan yi ga matasan mu masu tasowa. Bari in yaba muku kan rage zaman banza a jihar da ma kasa baki daya domin rashin aikin yi ne ke haifar da kalubalen tsaro da muke fama da shi a kasar nan. Inji Atiku

Ya kara da cewa, “Ina fata gwamnatin tarayya ta kwaikwayi abin da gwamnonin PDP da jahohin PDP suke yi a kasar nan, domin a kowace jiha ta PDP za ka tarar ana gudanar da ayyukan raya ababen more rayuwa.

Ba zan iya tunawa da duk wasu ayyukan da APC ta kaddamar a jihohi ba. Don haka, mai girma gwamna, kusan kana shimfida hanyar dawowar jam’iyyar PDP a jihar nan da ma kasa baki daya. Ina so in yaba gudummawar da kuka bayar game da hakan.”

A nasa jawabin, gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya ce aikin hanyar da gwamnatinsa ta dauka tare da aiwatar da shi yana cika alkawuran da ya dauka wa jama’a a lokacin yakin neman zabe.

Ya ce, “Mun zo nan ne domin kaddamar da titin Gombe-Maiduguri mai tsawon kilomita 4.2 a cikin babban birnin Bauchi. Wannan hanya ce mai ma’ana a bangarori da dama, na farko kamar kowace hanya, za ta inganta ayyukan tattalin arziki da za su inganta rayuwar jama’a.

“Na biyu, ci gaban Al’umma da inganta kyawun babban birnin jihar don haka, zai kara kusantar da mu wajen cimma shirin muhallin da muka yi niyyar samar da birnin Bauchi Zuwa matakin zamani.

Ya ce a lokacin da ya hau mulki a shekarar 2019, ya yi alkawura da dama bisa tsarin raya kasa mai taken: “My Bauchi Project” wanda ya tsara kudirinsa na daukar jihar Bauchi Zuwa matakin alkarya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *